BBC navigation

Fatou Bensouda na ziyarar wata majami'a da aka tafka tashin hankali a Kenya

An sabunta: 26 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 16:20 GMT
Fatou Bensuda

Fatou Bensuda na ziyara a Kenya

Babbar mai shigar da kara ta kotun hukunta manyan laifuka ta duniya wato ICC- za ta ziyarci wa ta majami'a dake yammacin Kenya, inda aka yi tashin hankali bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar shekaru biyar da su ka wuce.

Kusan mutane talatin ne suka rasu a lokacin da aka bankawa majami'ar wuta a Kiamba.

Babbar mai shigar da karar, Fatou Bensouda, ta koka a lokacin ziyarar ta a Kenya, a kan fargabar da wasu keda ita na bada shaida ga kotun ICC din, a kan manyan 'yan siyasa hudu a Kenyan.

Biyu daga cikin wadanda ake zarginsu da cin zarafin bil adama wato Uhuru Kenyatta da William Ruto, su na tunanin tsayawa takara a zaben shugaban kasar dake tafe a badi.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.