BBC navigation

Mahaukaciyar guguwa ta sa an soke kamfe a Amurka

An sabunta: 28 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 06:59 GMT

Irin barnar da guguwa mai suna Sandy ta yi a Cuba

Shugaban Amurka Barack Obama da abokin hamayyarsa Mitt Romney sun soke yakin neman zaben da suke yi a wasu yankunan kasar saboda yiwuwar aukuwar wata mahaukaciyar guguwa.

Shugaba Obama ya katse harkokinsa inda ya gudanar da taro ta wayar tarho da manyan jami'ai masu kula da ayyukan gaggawa don tattauna shirye-shiryen da aka yi na zuwan guguwar da za ta keta yankunan gabar ruwa na gabashin Amurka cikin wannan makon.

Masana yanayi sun yi kashedin cewa mahaukaciyar guguwar da aka sanyawa suna Sandy za ta iya zama mai matukar hadari - tana tafiya ne da yanayin tsananin sanyi tare da iska mai karfin gaske.

Jama'a dai za su so ganin yadda shugaba Obama zai bullowa lamarin.

Haka kuma za su so ganin irin martanin da Mitt Romney zai mayar idan guguwar ta auku.

Hakan ne ma ya sa jihohi irinsu NewYork, da Pennsylvania suka yi shelar dokar ta-baci.

Jama'a da dama kuma suka sayi abinci da ruwa don shirin fuskantar mahaukaciyar guguwar.

Masu nazari na ganin cewa wannan lamari zai yi tasiri a zaben shugaban kasar wanda za a gudanar nan da kwanaki goma masu zuwa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.