BBC navigation

An kashe mutane 80, in ji gwamnatin Burma

An sabunta: 28 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:30 GMT

Wasu yara da suka fake a sansanin 'yan gudun hijira sanadiyar rikicin Burma

Hukumomi a kasar Burma sun amince cewa an kashe fiye da mutane 80 tare da kone kauyuka da wasu sassan garuruwa a yammacin jihar Rakhine a rikicin da ake yi tsakanin mabiya addinin Buddha da musulmi 'yan kabilar Rohinya.

Dubban 'yan Rohinya din wadanda ake cewa ba 'yan kasa ba ne sun tsere daga yankin ta kananan jiragen ruwa.

Wani mai magana da yawun Shugaba Thein Sein ya ce an kara tsaurara matakan tsaro a jihar.

Sai dai wani wakilin kabilar Rohinya, Abu Taher, ya shaida wa BBC cewa kitsa hare-haren aka yi kuma sojojin kasar sun gaza kare jama'arsa.

Shi ma Babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya a kasar Burma, Ashok Nigam, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa, AFP cewar fiye da mutane dubu ashirin da biyu ne rikicin da aka yi a jihar Rakhine ya kora daga gidajensu, kuma akasarinsu musulmi ne.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.