BBC navigation

Dubban jama'a ne suka yi zanga-zanga a Spain

An sabunta: 28 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:50 GMT

Masu zanga-zanga a Spain

Dubu dubatar mutane sun shiga zanga-zangar baya-bayan nan da aka yi a kasar Spain don nuna adawa ga matakan tsuke bakin aljihu da gwamnati ta bayar da sanarwar dauka a kasafin kudi na shekara mai zuwa.

A Madrid, babban birnin kasar, gungun wasu masu zanga-zangar sun doshi Majalisar Dokokin kasar, amma 'yan sandan kwantar da tarzoma da shingayen da aka kakkafa suka hana su isa ginin.

Tun farko da rana, 'yan sanda dubu uku sun yi ta su zanga-zangar ta nuna rashin amincewa da zaftare kudaden da ake ba su na wasu hakkokinsu.

An kuma yi zanga-zangar a biranen Bercelona da Valencia da sauran wasu sassan kasar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.