BBC navigation

Ana ci gaba da samun rahotannin rikici a Syria

An sabunta: 27 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 18:17 GMT
Artabu a Syria

Ana ci gaba da rikici a Syria

An fuskanci karin tashin hankali a Syria a rana ta biyu da ya kamata a tsagaita wuta saboda bukukuwan babbar sallah.

Kuma wakilin BBC dake kan iyakar yace, an bada rahotannin harin bam da dakarun gwamnatin Syria su ka kai a birnenen Damascus da kuma Aleppo.

Ana cikin hakan ne kuma gidan talabijin na Syria ya bada rahoton fashewar wani bam da aka dana a mota a garin Deir Ezzor dake gabashin kasar

Abinda ke faruwa a Syria yanzu haka dai zai karayar da Lakhdar Brahimi mai shiga tsakani a rikicin, wanda ya yi fatan cewar kwarya-kwaryar tsagaita wutar zata taimaka wajen aza tubalin kwantar da tashin hankalin dake faruwa a Syria.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.