BBC navigation

Shugabannin coci na son a inganta tsaro a Najeriya

An sabunta: 29 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:27 GMT

Cocin da aka kai wa hari a Kaduna

Shugabannin coci-coci a Najeriya sun yi kira ga gwamnatin kasar ta inganta tsaro a wuraren ibada domin kaucewa yawan hare-haren da ake kai wa a kasar.

Shugabannin sun yi wannan kira ne bayan wani dan-kuna bakin-wake ya kai hari a wata coci a jihar Kaduna ranar Lahadi lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla takwas.

Gwamnatin kasar ta ce ta bai wa coci-coci da masallatai wadansu na'urori da za su iya hana kai hare-haren kunar bakin wake.

Sai dai Achbishop na Kaduna, Matthew Ndagosu, ya ce gwamnati ba ta samar musu da irin wadannan na'urori ba.

Ya ce: ''A rediyo na ji cewa an raba na'urorin amma babu wanda aka bai wa a cocin da nake jagoranta a Kaduna.Muna kira ga gwamnati ta kara bai wa sha'anin tsaro muhimmanci''.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.