BBC navigation

Obama ya gargadi Amerikawa kan mahaukaciyar guguwa

An sabunta: 29 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 20:35 GMT

Shugaba Obama ya yi gargadin cewa za a fuskanci kwanaki da dama na munanan abubuwa da za su biyo bayan aukuwar mahaukaciyar guguwar nan hadi da ruwan sama ta Sandy, wadda ta doshi gabar ruwan gabashin Amurka.

A wani jawabi da ya yi a fadar White House, Mr Obama ya ce yana da kwarin gwiwa cewa an dauki dukan matakan da suka dace domin shiryawa isowar guguwar ta Sandy.

Sai dai Mr Obama ya ce sako mafi muhimmanci da ya ke son mikawa jama'a shi ne cewa su bi umarni da shawarwarin da jami'an jihohi da na kananan hukumomi ke ba su.

Yace: "Idan sun ce ku tashi daga yankunan ku, to ku tashi kada ku bata lokaci".

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.