BBC navigation

Mahaukaciyar guguwa ta aukawa Amurka

An sabunta: 30 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:08 GMT

Guguwar Sandy ta tumbuke bishiyoyi

Wata mahaukaciyar guguwa dauke da ruwa kamar da bakin-kwarya ta aukawa gabashin Amurka inda ta haddasa ambaliyar ruwan da ba a taba fuskata ba a birnin New York.

Hukumomi a birnin sun ce igiyar ruwa ta yi tashin da ya wuce yadda aka yi hasashe.

Wasu hotunan talabijin sun nuna yadda ruwa ke toroko yayin da yake mamaye hanyoyi da lunguna na birnin.

Akalla mutane goma ne aka ba da rahotannin cewa sun rasa rayukansu a sassan da wannan mahaukaciyar guguwa ta aukawa.

Sassa da dama na kasar sun fada cikin duhu sanadiyar guguwar.

Lamarin dai ya sanya an dakatar da zurga-zurgar jiragen sama, da na kasa, da na motoci; an rufe makarantu, da kasuwar shunku ta birnin New York, abin da kwararru ke cewa zai janyo wa kasar asarar fiye da dala biliyan ashirin

Tun da farko sai da Shugaba Obama ya gargadi Amurkawa cewa za a fuskanci wahalhalu idan guguwar, wacce aka yi wa lakabi Sandy, ta iso kasar.

Shugaba Obama da abokin hamayyarsa sun dakatar da yakin neman zaben da suke yi sanadiyar tunkarowar da guguwar ta yi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.