BBC navigation

An daure mai safarar 'yanmata a Burtaniya

An sabunta: 30 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 12:30 GMT
Osezua Osolase

A filin jiragen sama na Stansted aka kama Osezua Osolase

An yankewa wani mutum mai amfani da tsafin "juju" a kan yara 'yanmatan da yake safara daga Najeriya zuwa Turai hukuncin daurin shekaru ashirin a gidan yari.

An shaidawa kotun Canterbury ta Burtaniya cewa mutumin mai shekaru arba'in da biyu da haihuwa, Osezua Osolase, ya kan yiwa marayun da talauci ya yiwa katutu alkawarin sama musu aiki amma sai ya saka su karuwanci a Turai.

Mai shari'a Adele Williams ta ce mai laifin ba shi da imani balle tausayi.

An samu Osolase da aikata laifuffuka biyar wadanda suka hada da safarar mutane, da fyade, da kuma cin zarafin kananan yara.

An shaidawa masu taimakawa alkali yanke hukunci cewa an yi amfani da "tsatsube-tsatsuben juju" irin na yankin Yammacin Afirka don jefa tsoro a zukatan uku daga cikin 'yanmatan da Osolase ya yi safararsu—daya daga cikinsu shekarunta goma sha hudu kacal.

Mai shari'ar ta ce mutumin, wanda ke dauke da kwayar cutar HIV mai karya garkuwar jiki, ya jefa 'yanmatan cikin wani yanayi na firgici da nufin tilasta su yi masa biyayya da kuma toshe bakinsu.

'Babu shakka kai mutum ne mara gaskiya...'

"Babu shakka kai mutum ne mara gaskiya ko kadan. Ga ka da girman-kai da taratsi, ba ka da imani, ba ka kuma da tausayi ga wadanda suka shiga hannunka"

Mai Shari'a

Mai shari'ar ta ce da Osolase: "Sana'arka ita ce ci-da-gumin wasu, da tursasa su, da kuma wulakanta su.

"Babu shakka kai mutum ne mara gaskiya ko kadan. Ga ka da girman-kai da taratsi, ba ka da imani, ba ka kuma da tausayi ga wadanda suka shiga hannunka".

Mai shari'ar ta ce Osolase ya mayar da 'yanmatan bayi wadanda yake sayarwa don su biya bukatar wadansu. Sannan ta ce fyaden da ya yiwa daya daga cikin 'yanmatan alhalin ya san cewa yana dauke da kwayar cutar HIV abu ne mai matukar muni.

Gidan Osolase dake Gravesend

A kan fara kai 'yanmatan gidan Osolase ne da ke Gravesend kafin daga bisani a tura su Turai don su yi karuwanci

An kuma bayar da shawarar mayar da Osolase kasarsa ta asali bayan ya kammala zamansa na kaso.

An dai shaidawa kotun cewa in an yi safarar 'yanmatan zuwa Burtaniya, a kan kai su gidan Osolase ne da ke Gravesend kafin daga bisani a tura su Turai don su yi karuwanci.

Yadda ake tsafe 'yanmata

Daya daga cikin 'yanmatan ta yi bayanin yadda aka yi mata tsatsube-tsatsuben juju a Najeriya. Yayin tsatsube-tsatsuben, a kan debi jinin yarinya sannan a yanki kadan daga cikin gashin kanta da na gabanta.

Daga nan sai a sanya ta ta yi rantsuwa cewa ba za ta fadawa kowa ba.

A filin jiragen sama na Stansted aka kama Osolase a watan Afrilu yana yunkurin hawa jirgin sama.

Lauyan da ke kare mai laifin, Anthony Orchard, ya ce bisa radin kansa Osolase ya bayyanawa 'yan sanda cewa yana dauke da kwayar cutar HIV.

Mista Orchard ya shaidawa kotun cewa: "Mista Osolase ya yarda ya aikata abin da ya aikata kuma ya yi nadama a bisa abin da ya biyo bayan safarar 'yanmata da ya yi daga Burtaniya, kuma a shirye yake ya rungumi hunkucin da aka yanke masa sakamakon hakan".

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.