BBC navigation

Yadda ake harhada sakamakon zaben Amurka

An sabunta: 30 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 14:50 GMT

Ta yaya BBC za ta bayar da rahoton sakamakon zaben shugaban kasar Amurka? Wannan jagora ya yi bayanin inda sakamakon zai fito, mecece kuri'ar jin ra'ayin masu zabe, da kuma yadda ake sanar da sakamakon jihohi.

Ta wacce kafa BBC ke samun sakamakon zaben?

A bana BBC za ta rika bayar da rahoto ne na sanarwar sakamakon jihohi kamar yadda tashar talabijin ta ABC ke bayarwa.

Idan tashar ta ABC ta bayar da sanarwa, to masu tattara sakamakon a ofishinmu na Washington za su shigar da alkaluman yawan 'yan tawagar masu zaben shugaban kasa da ko wanne dan takara ya samu.

Kamfanin dillancin labarai na Associated Press, wato AP, ne ke samar da dukkan sauran bayanan zaben, ciki har da sakamakon kuri'un da jama'a suka kada da sakamakon zaben Majalisar Dokoki.

Menene hasashen sakamakon?

Da farko sakamakon ka iya kasancewa hasashe, wanda aka yi ta hanyar tattara kuri'un jin ra'ayin masu zabe da/ko sakamakon zaben. Hakan na nufin za a bayyana sakamakon a matsayin hasashe har sai an kammala dukkan kuri'un da aka kada.

Dalilin hakan shi ne sau da yawa a kan sanar da cewa dan takara ya lashe jiha bisa la'akari da alkaluman da ba su kammala ba. Tsarin zabe na Amurka ya baiwa ko wacce jiha dama sakin wani bangare na sakamakon zaben tun kafin a kammala kidaya kuri'u. A kan tabbatar da sakamakon daga bisani idan aka kammala kidaya kuri'u.

A zabubbukan da 'yan takara ba sa tafiya kai-da-kai, ABC da ma sauran kafofin yada labarai na Amurka kan yi hasashen wanda ya yi nasara da zarar an rufe rumfunan zabe ta hanyar amfani da alkaluman kuri'ar jin ra'ayin masu zabe. Ga zabukan da 'yan takara ke tafiya kai-da-kai kuwa kafofin yada labaran kan jira har sai an samu alkaluma na zahiri. Jiran kan kai sa'o'i masu yawa ko ma tsawon dare.

Akan yi kuskure a hasashen?

E, musamman ma idan 'yan takara na tafiya kai-da-kai a zaben.

Mecece kuri'ar jin ra'ayin masu zabe?

Akan tattara kuri'ar jin ra'ayin masu zabe ne ta hanyar tambayar jama'a bayan sun kada kuri'a.

A bana kamfanonin Edison Media Research da Mitofsky International ne kadai za su gudanar da kuri'ar ta jin ra'ayin masu zabe.

BBC ba ta da hanyar samun cikakkun alkaluman kuri'ar jin ra'ayin masu zabe.

Shin Washington jiha ce?

A'a. Gundumar Colombia, wato DC, ba jiha ba ce, amma tana da kuri'u uku na tawagar masu zaben shugaban kasa. Ko da yake gundumar ba ta da 'yan majalisar dokoki nata na kanta, tana iya zaben shugaban kasa.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.