BBC navigation

Mahaukaciyar guguwa ta yi barna a Amurka

An sabunta: 30 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 19:21 GMT

Guguwar Sandy ta tumbuke bishiyoyi

An soma gagarumin aikin tattara komatsan da suka watsu a yankin kudu maso gabashin Amurka, bayan da guguwa mafi girma ta afkawa yankin cikin shekara da shekaru.

Magajin garin New York Michael Bloomberg yace an sake bude gadoji da kuma tituna, amma za a dauki wasu kwanaki kafin a dawo da hasken wutar lantarki da kuma harkokin sufuri

Wakilin BBC yace guguwar Sandy ta janyo asarar rayuka da dama, inda mutane 69 suka mutu a yankin Carribean, yayinda ake cigaba da samun wadanda suka mutu a nan
Birnin New Jersey inda guguwar ta afkawa, wata jaha ce da guguwar tayi wa barna.

Gwamnan Jahar Chris Christie yace ba ai tsammanin ganin irin barnar data auku ba.

Yace iskar mai karfin gaske ta tuzgo gidaje daga ginshikin su.

Ambaliyar ruwa kuma ta ci garuruwa.

A yanzu kuma guguwar ta matsa zuwa arewa maso yammaci, inda jahohin dake tsibiri ke shirin fuskantar cikkakken tasirin da iskar zata yi.

Fadar White house dai tace Shugaba Obama ya soke yakin neman zabensa na kwana na uku, domin ya sa ido akan aikin tattara komatsan da suka watsu.

Wata mahaukaciyar guguwa dauke da ruwa kamar da bakin-kwarya ta aukawa gabashin Amurka inda ta haddasa ambaliyar ruwan da ba a taba fuskata ba a birnin New York.

Hukumomi a birnin sun ce igiyar ruwa ta yi tashin da ya wuce yadda aka yi hasashe.

Wasu hotunan talabijin sun nuna yadda ruwa ke toroko yayin da yake mamaye hanyoyi da lunguna na birnin.

Akalla mutane goma ne aka ba da rahotannin cewa sun rasa rayukansu a sassan da wannan mahaukaciyar guguwa ta aukawa.

Sassa da dama na kasar sun fada cikin duhu sanadiyar guguwar.

Lamarin dai ya sanya an dakatar da zurga-zurgar jiragen sama, da na kasa, da na motoci; an rufe makarantu, da kasuwar shunku ta birnin New York, abin da kwararru ke cewa zai janyo wa kasar asarar fiye da dala biliyan ashirin

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.