BBC navigation

An kashe fitaccen mawaki a Somalia

An sabunta: 30 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:03 GMT

Wadansu makamai da aka kwace daga hannun 'yan kungiyar Al-Shabaab

Rahotanni daga kasar Somalia sun nuna cewa wadansu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun harbe har lahira wani shahararren mawakin kasar, Warsame Shire Awale.

Mista Awale ya yi aiki a gidan radiyo da ke Mogadhishu inda sau da dama yake rubutawa kana ya gudanar da wasannin kwaikwayon da ke yin kakkausar suka a kan kungiyar masu kaifin kishin Islama ta Al-Shabaab.

Ya yi fice wajen sukar manufofi da akidun kungiyar, yana zarginta da gurbata zukatan mutane da sunan Musulunci.

Kazalika ya yi fice a tsakanin matasan Somalia, wadanda yake kira da su kauracewa tashe-tashen hankula, inda maimakon hakan ya bukace su da su shiga makaranta.

Kungiyar 'yan jarida ta kasar ta ce Mista Awale ya yi ta samun sakonnin da ke barazana ga rayuwarsa saboda tsokacin da yake yi a kan kungiyar.

Ta kara da cewa shi ne dan jarida na goma sha takwas da aka kashe a kasar a cikin wannan shekarar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.