BBC navigation

Takaddama a kan magungunan zazzabin cizon sauro

An sabunta: 31 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 20:09 GMT
sauro

Zazzabin cizon sauro na illa a kasashe masu tasowa

Shirin samar da magungunan ciwon zazzabin cizon sauro kyauta ga marasa galihu a kasashe masu tasowa na ci gaba da janyo cece kuce tsakanin kungiyoyin kasa da kasa dake kula da lafiya.

Majalisar Dinkin Duniya tare da hadin gwiwar asusun yaki da cutar AIDS, da tarin fuka da kuma ciwon zazzabin cizon Sauron ke samar da magungunan ga kasashe takwas ciki kuwa har da Najeriya da Nijer da kuma Ghana.

Sai dai wasu kungiyoyin lafiya sun nemi ayi watsi da shirin saboda rashin tasirinsa yayinda wasu kuwa suka nuna goyon baya ga shirin.

Zazzabin cizon sauro na daga cikin cututtukan dake hallaka mutane da dame a kasashen Afrika musamman irinsu Najeriya da Nijer.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.