BBC navigation

An bude filayen Jirgin sama 2 a New York

An sabunta: 31 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:22 GMT

Mahaukaciyar guguwar Sandy

An bude biyu daga cikin filayen jiragen saman Birnin New York yayinda yayinda hukumomi a arewa maso gabacin Amurka ke aiki domin maido da muhimman ababen more rayuwar jama'a bayan barnar da gawurtacciyar mahaukaciyar guguwa dake tare da ruwa ta haddasa.

Jiragen sama sun sauka a filayen jirage na JFK da kuma Newark, filayen da suka fi hada hada a kasar.

Haka kuma an shirya za a bude kasuwar hannayen jari ta New York nan gaba kadan inda ake sa ran magajin garin Birnin Michael Bloomberg zai kada karaurawar bude kasuwar.

Bas - bas da kananan jiragen kasa na jigilar cikin gari da kuma jiragen ruwar sufuri tsakanin ungunisun koma aiki, to amma har yanzu jiragen karkashin kasa na birnin sun ci daga ba zama a rufe,saboda ruwan da ya kwarara cikin hanyoyin ya sa za a ci gaba da rufe su har wasu yan kwanaki masu zuwa.

Sai dai har yanzu gidaje da dama ba su da wutar lantarki, kuma za a cigaba da rufe hanyoyin jiragen kasa na karkashin kasa na birnin na New York.

Fiye da mutane arba'in ne suka rasa rayukan su a laokacin guguwar, kuma sha takwas daga cikin su mazauna birnin New York ne.

Ana sa ran Shugaba Obama zai kai ziyara a Jihar New Jersey.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.