BBC navigation

Gobara ta halaka mutane 25 a Saudiyya

An sabunta: 31 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 16:43 GMT

Rahotanni daga Saudiyya sun ce wata gobara da aka yi a wajen wani bikin daurin aure a gabacin kasar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla ashirin da biyar tare da raunata wasu talatin.

An ce wutar ta soma ne lokacin da wata na'urar rarraba wutar lantarki mai karfin gaske ta katse ta kuma fado kan gidan da ake bukin bayan albarusan da ake harbawa sama domin murna a lokacin bukin suka same ta.

Kakakin rundunar tsaro ta Civil Defence a kasar ya shedawa gidan Talabijin na Al-Arabiyya cewa galibin wadanda suka mutun mata ne dake halartar bukin, koda yake akwai maza da yara a cikinsu.

Yace gwamnan yankin ya umurci hukumomi da su kaddamar da bincike kan lamarin a daidai lokacin da ake kokarin gano ko su wanene su ka mutun.

Rahotanni sun ce akwai daruruwan mutane a cikin gidan lokacin da abin ya auku; kuma tuni aka kai wadanda suka ji rauni asibiti.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.