BBC navigation

Za a karashe aiki kan tsarin mulkin Masar nan bada jimawa ba

An sabunta: 28 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:16 GMT
Kotun kolin Kasar Masar

Kotun kolin Kasar Masar

Yayin da ake ci gaba da zanga-zanga a Masar a kan dimbin ikon da Shugaba Mursi ya bai wa kansa, daya daga cikin manyan kotunan kasar ta yi kakkausar suka a kan shugaban.

Kotun tsarin mulki ta zargi kungiyar 'Yan'uwa Musulmi da diyanta ne suka fi yawa a gwamnatin kasar, da neman yin ramuwar gayya a kan hukunce-hukuncen da kotun ta yanke a can baya.

A wajen wani taron manema labarai a birnin Alkahira mai magana da yawun kotun tsarin mulki ta kasar, Maher Samy ya ce, alkalai ba za su bada kai ba a kan duk wata takura.

Ya ce, kotun kolin kasar Masar ba za ta amince da duk wani ta'addanci ko wata barazana ba, kuma ba za ta yadda da matsin lamba daga kowa komai karfinsa ba.

Ya ci gaba da cewar a shirye kotun koli ta ke ta tunkari wannan batu komai zai faru ko da kuwa alkalanta za su rasa rayukansu ne.

An dai ci gaba da ba-ta-kashi a birnin Alkahira, an kuma shirya yin wasu sabbin zanga-zanga a kwanakin da ke tafe.

Watakila kuma majalisar tsarin mulki ta fiddo da wani sabon tsarin mulkin da gaggawa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.