BBC navigation

Isra'ila ta kulli shawarar hambarar da Shugaba Abbas na Palasdinu

An sabunta: 14 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:09 GMT
Shugaba Mahmud Abbas

Shugaba Mahmud Abbas

Wata takarda daga ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila da aka tsegunta ta bada shawarar kifar da shugaban Palasdinwa Mahmud Abba muddin aka amince da bukatar mahukuntan Palasdinawan na Palasdinu ta zama mamba 'yar kallo a majalisar dinkin duniya.

Takaddar wadda BBC ta samu ta ce mai yiwuwa wargaza gwamnatin Palasdinawan shi ne kadai zabin da suke da shi idan har kokarin da suke na hana ta zama mamba ya ci tura.

Wakilin BBC ya ce, sai dai kuma kiraye kirayen kifar da shugaban Palasdinawan Mahmud Abbas ya tada tambaya kan kowa ye zai maye gurbinsa.

Babban mai shiga tsakanin na Palasdinawa, Saeb Erakat ya shaidawa BBC cewa mahukuntan Palasdinu sun dauki barazanar Isra'ilan da gaske kuma za su iya yin wani yunkuri na hallaka shi.

Ranar 20 ga watan Nuwanba ne Shugaba Mah mud Abbaa zai mikawa majalisar dinkin duniya bukatar neman Palasdinu ta zama mamba mara cikakken iko a majalisar.

Matakin da Isra'ila da Amurka dai ba sa goyon baya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.