BBC navigation

Wata mata ta radawa 'ya'yan sunayen Obama da Romney a Kenya

An sabunta: 7 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:37 GMT
Obama da Romney na Kenya

Obama da Romney na Kenya

Wata maata a kasar Kenya, ta haifi 'yan tagwaye biyu maza a yau, da aka sake zaben shugaba Obama a wa'adin mulki karo na biyu.

Ta sawa 'ya'yan sunan Obama da kuma abokin karawarsa na jam'iyyar Republican, Mitt Romney.

Matar mai suna Millicent Owuor ta haifi tagwayenne a wani asibiti dake yammacin Kenya, wanda ke kusada da kyauyen kakkannin Mista Obama dake Kogelo.

An dai yi ta bukukuwan nasarar da Obaman ya samu a yankin.

Matar ta dauki hoto tare da jariran nata biyu.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.