BBC navigation

'Yan adawar Masar na zanga zanga kan tsarin mulkin Morsi

An sabunta: 30 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:02 GMT
Majalisar rubuta tsarin mulkin Masar

Majalisar rubuta tsarin mulkin Masar

Masu zanga zanga a birnin Alkahira na Kasar Masar sun ci gaba a duk tsawon rana, a kan Shugaba Mohammed Morsi da kuma dangane da sabon daftarin kundin tsarin mulki da majalisar da ta tsara rubuta shi ta gaggauta amincewa da shi.

Shugaba Morsi da kansa ya fuskanci masu zanga zangar a lokacin da ya halarci sallar juma'a a wani masallaci dake birnin Alkahira

Masu zanga zangar da suke sukar sabon ikon da ya baiwa kansa na cike da fushin cewar an gaggauta kammala daftarin tsarin mulkin a cikin sa'oi 16 kachal.

Wakilin BBC yace manufar hakan kuma shi ne don su takawa kotuna birki kada su kalubalance su, wadanda suma suke adawa da sabon ikon da Shugaba Morsin ya baiwa kansa.

Za dai a gudanar da ƙuri'ar raba gardama kan daftarin tsarin mulkin bayan Shugaban ƙasa ya amince da shi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.