BBC navigation

Sojin Najeriya sun soki rahoton kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Amnesty

An sabunta: 1 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 16:50 GMT
Tambarin Amnesty International

Tambarin Amnesty International

Hukumar Sojin Najeriya ta bayyana rahoton kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Amnesty International a matsayin wani abun shirme da aka yi shi domin neman kudi.

Da yake mayar da martani kan rahoton kungiyar ta Amnesty, mai magana da yawun rundunar, Kanar Mohammed Yarima ya ce, rahoton ba na kwarai ba ne, kuma babu gaskiya a cikinsa.

Ya kuma musanta cewar jami'an rundunar na aikata miyagun ababuwa da suka hada da duka da fyade da ma kisa.

Kanar Sagir ya ce, dukanin mutanen da jami'an rundunar suka kama su kan bincike su ne domin tabbatar da cewar ba su da laifi, kuma suna sakin wadanda suka samu ba su da laifin.

Haka kuma ya ce, suna mika wa yansanda wadanda ake zargin suna da laifi domin gurfanar da su a gaban kumliya.

Shi dai rahoton da kungiyar kaare hakkin dan adam ta Amnesty International ya fitar a Najeriya ya zargi sojojin kasar da cin zarafin bil adama a yakin suke yi da kungiyar 'yan kishin Islamar nan ta Boko Haram.

Amnesty tace,sojojin na wuce-gona da iri a yakin da suke yi da sojin sa kan - inda ta ce suna gaana wa mutane akuba da kisa ba tare da shari'a ba, da kone gidajen mutane da kuma tsare mutane ba tare da gurfanar da su gaban kotu ba.

Kungiyar tace, an jefa mutane cikin wani hali na tsaka mai wuya, kasancewar dukkan bangarorin biyu suna aikata ayyukan ashsha ne.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.