BBC navigation

Majalisar dinkin duniya ta gaza matuka a Sri Lanka

An sabunta: 13 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:07 GMT
Fararen fatar da aka kashe a Sri Lanka

Fararen fatar da aka kashe a Sri Lanka

Wani rahoto da MDD ta hada, wanda kuma BBC ta samu kofe, ya ce Majalisar ta gaza matuka wajen bada kariya ga fararen hula a matakin karshe na yakin basasar Sri Lanka, shekaru 3 da rabi da suka wuce.

Wakiliyar BBC ta ce rahoton, ya ce manyan jami'an Majalisar dinkin duniya dake birnin Colombo ba su dauka cewa hakkinsu ne su hana aukuwar kisan fararen hular ba.

Kiyasin da Majalisar ta yi dai ya nuna cewa akalla mutane dubu 40 ne aka kashe a watannin karshe na yakin basasar.

Rahoton ya kuma soki lamirin matakin da MDDr ta dauka na kin wallafa adadin fararen hular da aka kashe, kuma janye ma'aikatan ta da Majalisar ta yi daga yankunan da ake yaki, ya janyo nakasu ga shirin kare fararen hula.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.