BBC navigation

Ana tafka mummunan fada a Syria

An sabunta: 30 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 10:59 GMT
Wani hari a Syria

Wani hari a Syria

Akwai rahotannin anyi mummunan taho - mu - gama a Damascus babban birnin Kasar Syria, a wuraren filin jirgin sama da kuma a lardunan gabashin Kasar.

Al'amarin ya auku ne bayan harkokin sadarwa a kasar sun gamu da cikas

An dai rufe Babban titin daya dangana zuwa filin jirgi, an kuma dakatar da tashin jirage tunda safiyar yau

Wani wakilin BBC a Damascus ya ce layukan wayoyin gida dana Salula, duk sun gamu da cikas a daukacin Kasar.

Ga alamu kuma ana tafka kazamin fada a kusa da filin jirgi na Damascus.

Gwamnatin Syria dai ta ce, 'yan ta'adda ne suka katse layukan sadarwar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.