BBC navigation

Mutane miliyan biyu da rabi ke gudun hijira a cikin Syria

An sabunta: 13 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:18 GMT
Yaran da aka raba da gidajensu a Syria

Yaran da aka raba da gidajensu a Syria

Babbar kungiyar agaji ta Syria, ta ce yanzu akalla mutane miliyan 2 da rabi ne aka tabbatar cewa sun fice daga muhallinsu a cikin kasar.

Wannan adadi dai da kungiyar Red Cross ko Croix Rouge ta Syriar ta bayar, ya ninka har fiye da sau 2, kiyasin da aka yi tun farko.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya ta ce adadin ya nuna cewa jamaa na cigaba da buya a cikin kasar, kuma da dama daga cikinsu sun fice daga muhalinsu fiye da sau daya.

Wakiliyar BBC duk da cewa majalisar dinikin duniya ta sha gabatar da bukata ga gwamnatin Syriar domin ta kyale karin ma'aikatan agaji shiga cikin kasar, amma har yanzu, rawar da take takawa a cikin kasar ta Syria, takaitacciyar ce inda a wasu lokutan ma yake zame ma ta dole ta dakatar da cibiyoyin da suka fara aiki, sakamakon fadan da ake yi tsakanin sojojin gwamnati da dakarun 'yan tawaye.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.