BBC navigation

Turkiya ta nemi NATO ta samar mata da makaman kakkabo makamai masu linzami

An sabunta: 21 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:22 GMT
Sakatare Janar na Kungiyar NATO, Anders Rasmussen

Sakatare Janar na Kungiyar NATO, Anders Rasmussen

Kungiyar tsaro ta NATO ta ce Turkiyya ta bukace ta da ta girke makaman kariya masu linzami sampurin Patriot a yankin kasarta, kusa da kan iyaka da Syria.

Sakatare Janar na NATO, Anders Fogh Rasmussen kenan, lokacin da yake bayyana hakan.


Ya ce girke makaman zasu taimaka wa Turkiyya wajen kare al'umar kasarta da yankunanta , kuma kawancen zai tattauna kan wannan bukata ba tare da wani jinkiri ba.


Turkiya ta koka kan yadda makamai ke fadawa cikin yankin kasarta daga Syria, yayinda rikici a can ke kara ta'azzara, inda ita ma ta harba makamai cikin Syriar a matsayin martani.


Cikin watan Oktoba an kashe wasu fararen hula 'yan kasar Turkiya su biyar, lokacin da wani makamin iggwa da aka harba daga Syria ya fada kan wani kauyen Turkiyya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.