BBC navigation

An samu karuwar gurabun aikin yi a Amurka gabanin zabe

An sabunta: 2 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:00 GMT
Wata cibiyar neman aiki a Amurka

Wata cibiyar neman aiki a Amurka

Rahoto na baya-bayan da aka fitarwa kowanne wata a kan guraben ayiki a Amurka, ya nuna cewa an samar da sabbin guraben ayyukan yi fiye da dubu dari da 70 a cikin watan jiya, fiye da yadda aka yi tsammani.

Sai dai har yanzu adadin marasa aikin yi yana da yawa.

Fadar Shugaban Kasa ta White House ta ce rahoton ya nuna cewar tattalin arzikin Amurka na ci gaba da murmurewa daga mummunan koma bayan da ya samu tun bayan babban koma bayan tattalin arzikin duniya na 1929.

Dantakarar Shugaban kasar Amurka a Jama'iyar Republican, Mitt Romney ya ce, alkaluman wani tunin bakin ciki ne na cewar har yanzu tattalin arzikin na nan kusa tsaye cik.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.