BBC navigation

An sasanta tsakanin gwamnonin da fadar shugaban Najeriya

An sabunta: 1 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:12 GMT
jona

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan

A Najeriya, gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohin kasar sun ce sun samo hanyar daidaitawa dangane da gardamar da suke yi da juna a kan asusun rarar man fetur.

A baya dai wasu gwamnonin sai da suka shigar da karar gwamnatin tarayyar a kotu cewa ba su yarda da ci gaba da rike rarar kudin man fetur da sunan ajiya don gobe ba.

Amma daga baya sai suka ce za su sasanta da juna a wajen kotu.

Gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako ya shaidawa wakilinmu a fadar gwamnatin Najeriya, Ibrahim Isa cewar sun cimma daidaito kuma nan bada jimawa ba za a kasafta wani abu daga cikin kudin na rarar man fetur.

Batun kudin rarar man fetur a baya ya janyo bangaren gwamnonin jihohin kasar gabatar da kokensa gaban kuliya saboda gwamnatin Tarayya ta ki raba musu kudin.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.