BBC navigation

An saki matuka jirgin ruwan da aka sace a Najeriya

An sabunta: 1 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 16:10 GMT

Wani kamfanin mai na Faransa, mai suna Bourbon, ya ce an saki ma'aikatan jirgin ruwansa da aka sace a gabar teku da ke yankin Neja Delta na Najeriya.

Kamfanin ya ce ma'aikatan -- 'yan kasar Rasha guda shidda da kuma dan Estonia daya -- na cikin koshin lafiya.

"Duk da irin haalin kuncin da su ka shiga ciki a lokacin da ake tsare da su, da alama su na cikin koshin lafiya," inji kamfanin.

Ya ce jami'an tsaro, wadanda suka hada harda hukumar hadin-gwiwar tsaro na soji, wato JTF, sun yi aiki wajen ceto ma'aikatan.

Kakakin hukumar JTF, Kanar Onyema Nwachukwu, ya ce dakarunsu na daga cikin wadanda su ka taimaka wajen aikin.

Yace: "Tabbas dakarunmu na cikin wadanda su ka bi dukkan lungunan yankin Neja Delta domin tabbatar da ganin cewa an sako mutanen ba tare an ji masu rauni ba.

"To amma ba za mu ce komai a kan batun kudin fansa ba ko kuma cikakken bayani kan yadda aka yi aikin ceto su ba".

A baya dai an yi garkuwa da mutane da dama a yankin na Neja Delta mai arzikin mai na Najeriyar.

Sai dai bayanai sun nuna cewa shirin afuwar da aka yi wa masu fafutuka a Neja Deltan a shekarar 2009 ya taimaka wajen rage yawan garkuwa da mutanen da ake yi a yankin.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.