BBC navigation

Obama na shirin cigaba da yakin neman zabe

An sabunta: 1 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:05 GMT
Obama da tawagarsa

Obama da tawagarsa

A yau ne shugaba Barack Obama ke komawa yakin neman zabe, bayan da ya dakatar da shi na tsawon kwanaki ukku, sakamakon mahaukaciyar guguwar da ta ratsa ta wasu sassa na Amurka, inda ta haddasa barna mai matukar yawa ta dukiya da kuma rayuka.

Mazauna yankin arewa maso gabashin Amurka su na daukar matakai na kokarin cigaba da harkokinsu kamar yadda suka saba bayan mahaukaciyar guguwar.

Nan gaba a yau ne, ake sa ran bude babban filin jiragen sama na birnin New York, da kuma takaitaciyyar zirga-zirgar jiragen kasa a layukan dogo na karkashin kasa wanda ambaliyar ruwa ta lalata.

Tun a jiya ne dai dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Republican, Mitt Romney ya koma yakin neman zabensa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.