BBC navigation

An kashe mutane da dama a Maiduguri

An sabunta: 2 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:54 GMT
Birnin Maiduguri, jihar Borno a Najeriya

Birnin Maiduguri,jihar Borno a Najeriya

Rahotanni daga Maiduguri da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa, an kashe mutane da dama a wasu yankuna na garin a jiya Alhamis.

Wasu da aka kashe musu dangi sun ce akasarin wadanda aka kashe din matasa ne, sun kuma yi zargin cewa sojoji ne suka yi kashe-kashen bayan sun ware matsa daban tsofaffi daban.

Mazauna birnin Maiduguri daban-daban sun shaida wa BBC cewa, unguwannin da aka gudanar da kashe-kashen a cikinsu sun hadar da Kalari, Sabon lamba, gwange da kuma Gamborou.

Sai dai mai magana da yawun rundunar hadin gwiwa da ake aikin samar da zaman lafiya a Maidugurin JTF ya ce ba shi da labarin kashe-kashen amma zai bincika ya kuma yi karin bayani nan gaba, yayin da kakakin rundunar 'yan sandan jihar ya ce yana da labarin afkuwar lamarin amma sai nan gaba zai yi karin bayani.

Jami'an tsaro a Maidugurin dai na cewa, 'ya'yan kungiyar Jama'atu Ahlussunah Lidda'awati Wal Jihad na fakewa ne a tsakankanin al'ummar birnin suna kaiwa jami'ansu hari, kuma mazauna garin ba sa basu hadin kai wajen nuna maharan.

Su kuwa wasu mazauna garin na cewa an sa su ne a tsaka mai wuya, saboda idan suka nuna maharan, daga bisani 'yan uwansu ne suke dawowa su kashe su bayan sojoji sun tafi.

Wadannan kashe-kashen da mazauna Maidugurin ke cewa an yi sun faru ne a ranar da kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta fitar da wani rahoto da ke cewa jami'an tsaron kasar kan wuce gona da iri a fadan da su ke yi da kungiyar Jama'atu Ahulus Sunna Lidda'awati wal jihad da aka fi sani da suna Boko Haram.

Sai dai jami'an tsaron sun musanta zargin cewa suna kisan gilla ko wuce gona da iri a martanin da suke mayarwa a hare-haren da kungiyar ta Boko Haram ke kaiwa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.