BBC navigation

'Yan tawaye a Syria sun hallaka daruruwan dakarun gwamnati

An sabunta: 2 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:50 GMT
Dakarun 'yan tawayen kasar Syria

Dakarun 'yan tawayen kasar Syria

Wani hoton bidiyo da aka saka a shafin internet ya nuna yadda 'yan tawayen kasar Syria ke hallaka daruruwan dakarun gwamnatin da suka cafke, bayan da suka mamaye shingayen bincike dake arewacin kasar.

Hotunan bidiyon sun nuna yadda 'yan bindigar ke yin kabbara Allahu Akbar suna kuma kwallo da fursunonin dake birgima a kasa, inda daga bisani aka ji karar bindiga mai sarrafa kanta da kuma ganin gawawwaki a warwatse.

Lamarin dai ya haifar da yin Allawadai daga masu fafutukar kare hakkin biladama.

An dai zargi kungiyar nan mai kaifin ra'ayin addinin Islama da hannu a cikin afkuwar lamarin, inda rahotannin da suka biyo baya ke cewa mayaka 'yan tawaye sun kwace shingayen bincike dake kan manyan hanyoyin kudu maso arewacin birnin Aleppo.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.