BBC navigation

Uganda za ta janye sojojin ta daga Somalia da Congo da kuma Jumhuriyar Afurka ta Tsakiya

An sabunta: 2 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 19:40 GMT
Dakarun Uganda

Uganda zata janye dakarun ta daga wasu kasashen Afirka

Ministan tsaron cikin gida na Uganda, Muruli Mukasa, ya ce kasar sa za ta janye sojojin ta daga Somalia da Jumhuriyar Demokradiyyar Congo da kuma Jamhuriyar Afruka ta Tsakiya

Wakiliyar BBC ta ce idan har Ugandan ta janye sojojinta daga wadannan kasashe uku, to hakan ba karamar illa zai yi ba ga kokarin da ake yi na wanzar da zaman lafiya a yankin.

A makon jiya ne dai Uganda ta ce tana shirin janye sojojinta daga kasashen saboda wani rahoton Majalisar dinkin duniya ya yi zargin cewa Ugandar na goyon bayan 'yan tawayen Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

Ministan dai bai bada takamaimai lokacin da dakarun za su janye ba.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.