BBC navigation

Magajin Garin birnin New York ya marawa Obama baya

An sabunta: 2 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 08:09 GMT
Shugaba Obama da abokin karawarsa Mitt Romney

Shugaba Obama da abokin karawarsa Mitt Romney

Magajin Garin birnin New York, Michael Bloomberg, ya marawa shugaba Obama baya wajen sake lashe zabe, sakamakon mahaukaciyar guguwar nan da ta haifar da fargaba a arewa maso gabashin Amurka.

Mr Bloomberg tsohon dan jam'iyar Republican ne da yanzu haka ya zama dan siyasa mai zaman kansa.

Ya sha sukar Mr Obama da abokin karawarsa Mitt Romney dake shirin fafatawa a cikin makon gobe, amma kuma ya ce ya yanke shawarar cewa Mr Obama ne dan takara mafi cancanta wanda zai iya shawo kan matsalar sauyin yanayi a duniya.

Shugaba Obaman dai ya ci gaba da yakin neman zabe a ranar Alhamis, bayan shafe kwanaki biyun da yayi wajen maida hankalinsa kan matsalolin da mahaukaciyar guguwar nan ta Sandy ta haifar a yankin arewa maso gabashin kasar.

Ya gudanar da gangamin yakin neman zaben ne a jihohin Wisconsin, Nevada da Colorado, yayinda abokin karawarsa na jam'iyar Republican, Mitt Romney ya gudanar da nasa a jihar Virginia.

Yayinda yake gabatar da jawabi a wajen gangamin yakin neman zaben yankin Brown Cony dake jihar Wisconsin, Mr Obama ya ce Amurka za ta maida hankalinta ne kan abinda ya fi yiwa kasar baki daya alfanu, inda ya ce ba a bukatar wata babbar ajanda ta gwamnati, ko kuma karamar ajanda ta gwamnatin, ana bukatar tsaka-tsakin ajanda ce kan aiki tukuru wacce ke la'akari da cewa idan aka ilmantar da yara marasa galihu zai kawo ci gaba ga kasa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.