BBC navigation

Aski ya zo gaban goshi a zaben shugaban Amurka

An sabunta: 4 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:08 GMT
Aski ya zo gaban goshi a zaben Amurka

Obama da Romney

Shugaba Obama da abokin hamayyarsa Mitt Romney na jam'iyyar Republican suna cigaba da yakin neman zabe a jihohin da ake ganin suna da muhimmanci wajen samun nasara a zaben da za a yi a Amurka ranar Talata.

Lokacin da yake magana a gangami na jam'iyyar Democrat a jihar Virginia tsohon shugaban kasar, Bill Clinton, ya ce Mista Obama ya taka rawar gani a wa'adin mulkinsa na farko idan aka yi la'akari da matsalolin da kasar ta fuskanta lokacin da ya zama shugaban kasa.

Mista Romney ya shaida wa wani gangami a Colorado cewa shi ne zai zamo shugaban kasar da zai yi watsi da bambancin siyasa, ya jagoranci jam'iyyun na Republican da Democrat, ya kuma dora tattalin arzikin kasar kan hanyar da ta dace.

A jihar Ohio shugaba Obama ya ce an samu ci gaba a shekaru hudun da suka wuce, amma har yanzu da sauran aiki.

Ya ce: " Za mu cigaba da gwagwarmayar da muke yi saboda mun san kasar nan ba za ta bunkasa ba, kuma ba za ta yi nasara ba, muddin ba a gina mutane masu karamin karfi ba''.

An yi zanga-zanga

A birnin Washington, daruruwan mutane ne suka gudanar da zanga-zanga don nuna goyon bayansu wajen ganin gwamnati ta ci gaba da daukar nauyin shirye-shiryen da ta kan dauka na gidajen radiyo.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun shiga taron gangamin ne da aka kira Million Puppet March da siffofin da wasu kan fito da su a wasannin yara da ake kira "Sesame Street", shirin da gwamnati ce ke daukar nauyinsa.

Wadannan mutane sun je Majalisar Dokokin Amurka ne domin mayar da martani ga dan takarar shugancin Amurka a karkashin jam'iyar Republican, Mitt Romney, wanda ya sha alwashin daina bayar da kudin da gwamnati ke fitarwa don daukar nauyin wadansu shirye-shirye a kafafen watsa labarai na PBS da NPR idan ya zama shugaban kasa.

Ita dai jam'iyar Republican ta ce dole ne ta zaftare kudaden da ake kashewa a Amurka, ganin yadda ake ci gaba da samun gibi a kasafin kudin kasar, don haka ne ma take son dakatar da daukar nauyin irin wadannan kafafen watsa labarai.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.