BBC navigation

Ms Suu Kyi bata goyan bayan masu fada a Burma

An sabunta: 3 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:10 GMT
Jagorar 'yan adawa ta kasar Burma

Jagorar 'yan adawa ta kasar Burma

Jagorar 'yan adawa a Kasar Burma, Aung San Suu Kyi, ta yi kira ga bangarorin dake rikici a yammacin kasar da su yi hakuri da juna, amma ta ki daukar wani matsayi a kan makomar musulmai 'yan kabilar Rohingya--- wadanda aka tilastawa dubbansu barin gidajansu.

Ms Suu Kyi ta shaidawa BBC cewa baza ta yi amfani da matsayinta ba wajan yada manufofin 'yan kabilar Rohingya ba tare da sanin ainahin musabbabin matsalar ba.

Kusan mutane casa'in ne aka tabbatar sun rasa rayukansu a rikicin kabilanci na baya-bayannan da akai a jahar Rakhine.

A wani labarin kuma shugaban hukumar tarayyar Turai, Jose Manuel Barroso, ya taso da maganar makomar 'yan kabilar Rohingya a lokacin tattaunawarsa da shugabannin kasar Burma, ciki har da Aung San Suu Kyi, a Naypyidaw, babban birnin kasar.

Har ila yau a ganawarsa da shugaba Thein Sein, Mr Barroso ya yi alkawarin ba kasar tallafin dala miliyan dari domin ayyukan ci gaban kasa, sun kuma tattauana kan yadda za'a habaka cinikayya tsakaninsu.

Mr Barroso dai shi ne wani jami'i daga kasashen yamma na baya bayannan da ya kai ziyara kasar Burma tun bayan da gwamnatin kasar da sojojin ke marawa baya ta fara aiwatar da wasu sauye-sauye a kasar bara.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.