BBC navigation

uganda za ta janye sojinta daga Somaliya

An sabunta: 3 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 06:04 GMT

Sojin Uganda

Gwamnatin kasar Uganda ta ce za ta janye dakarunta daga kasar Somalia da Jamhuriyyar Dimokradiyyar Kongo da kuma Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.

Ministocin kasar guda biyu da suka hada da Firaministan Kasar da Ministan tsaro, sun ce janye dakarun, mayar da martani ne ga wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya wanda yayi zargin cewa Uganda ta na taimakawa 'yan tawaye a Jamhuriyyar Dimokradiyyar Kongo.

Uganda ta bayyana rahoton a matsayin abin takaici.

Ministocin ba su bayyana lokacin da za a janye dakarun baki daya ba.

Wakilin BBC a Kampala babban birnin kasar yace janyewar ka iya yin mummunar illa ga aikin samar da zaman lafiya a Somalia.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.