BBC navigation

Mahaukaciyar guguwa ta haddasa karancin man fetur

An sabunta: 3 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 05:56 GMT

Karancin manfetur a wasu sassa na Amurka

Mahaukaciyar guguwa da aka lakabawa suna Sandy ta haddasa karancin man fetur da diesel a yankunan da ta yi barna.

Halin da mazauna yankunan suka shiga na taraddadi da damuwa ya fusata su.

Wannan dalilin ne ya sa shugaba Obama ya bada umarnin cewa a samar da miliyoyin litocin man fetur ga yankunan.

Mr Obama da abokin karawarsa Mitt Romney, sun shiga kwanaki uku na karshe a yakin neman zabensu, kafin ranar Talata inda za a gudanar da zaben shugaban kasar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.