BBC navigation

'Yan tawayen Mali za su gana da Compaore

An sabunta: 5 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 14:17 GMT
shugaban_burkina_faso_blaise_compaore

Shugaban Burkina Faso Blaise Compaore

Ana sa ran shugaban kasar Burkina Faso, Blaise Compaore, zai gana da shugabannin kungiyar masu Tsattsauran ra'ayin addinin Islama ta Ansar Dine ranar Talata, a wani yunkuri na kawo karshen rikicin Mali.

Wakilan kungiyar ta Ansar Dine sun dai isa Ouagadougou ne, babban birnin kasar Burkina Faso, ranar Juma'a, inda suka yi ganawar minti arba'in da biyar da ministan harkokin wajen kasar, Tieman Coulibaly.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa gwamnatin kasar na sanya matsin lamba a kan Ansar Dine, daya daga cikin kungiyoyin masu fafutukar da ke iko da arewacin Mali, da su yanke alaka da kungiyar Al-Qaeda.

Ansar Dine dai ta hade da kungiyoyi masu kaifin kishin Islama ne irin su Al-Qaeda domin su mamaye arewacin Mali.

''Komai ya tafi daidai'', a cewar shugaban wakilan kungiyar, Algabass Ag Italla.

'Za mu ba da hadin-kai'

Wakilan na Ansar Dine sun ce a shirye suke su bayar da hadin-kai don nemo hanyar da za a bi wajen kawo karshen rikicin ta hanyar tattaunawa, kamar yadda wata majiya ta fada.

Shugaban wakilan kungiyar ta Ansar Dine ya shaidawa AFP cewa ya gana da ministan harkokin wajen Mali a kan batun da ya shafi gwamnatin rikon kwaryar kasar, sai dai bai bayyana abin da tattaunawar ta kunsa ba.

Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma, wato ECOWAS, mai mambobi goma sha shida ta bukaci Ansar Dine ta kawo karshen ta'addaci da aikata miyagun laifuffuka a yankin, ta kuma yanke alaka da kungiyar Al-Qaeda da sauran kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayin addinin Islama ta kuma shiga cikin tattaunawar siyasa domin kawo zaman lafiya a kasar ta Mali.

Da yake mayar da martani, Intalla ya ce Ansar Dine ba ta karbar umurni daga kowacce kungiya.

Ya kuma kara da cewa a shirye suke su tattauna domin a samu zaman lafiya.

Kasashe makwafta na jin tsoro

Kasashen da ke makwabtaka da Mali da kuma kasashen ketare na jin tsoron kasar na iya zama sansanin 'yan ta'adda.

Ranar Juma'ar da ta gabata, Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya bukaci kungiyar ECOWAS ta dauki mataki a kan kungiyar Al-Qaeda, da safarar miyagun kwayoyi, da sace jama'a domin yin garkuwa da su da kuma sauran muggan laifuffuka wadanda suka sanya arewacin Mali ya zama sansanin 'yan ta'adda.

Kamfanin dillancin labaran kasar Algeria ya ce wata majiya ta kusa da gwamnati ta ce masu yawan shakatawa a tsorace suke; hakan ya sanya gwamnatin kasar ta nemi tattaunawa da wakilan kungiyar Ansar Dine, amma gwamnatin kasar ba ta ce komai ba a kan hakan.

"Ana kallon Algeria a matsayin wata kasa wacce za ta taka muhimmiyar rawa wajen magance rikicin, kuma a makon da ya gabata sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, ta ziyarci kasar tare da neman hadin kan ta don a kawo karshen rikicin na Mali."

Ana kallon Algeria a matsayin wata kasa wacce za ta taka muhimmiyar rawa wajen magance rikicin, kuma a makon da ya gabata sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, ta ziyarci kasar tare da neman hadin kan ta don a kawo karshen rikicin na Mali.

Algeria na janye jikin ta daga shiga duk wani abu da ya shafi kasashen ketare, hakazalika Washington na ganin da karfin ikon sojojinta, da kwarewarta a harkar yaki da ta'addanci da kuma hukumomin leken asiri za ta iya taka rawa a cikin al'amarin.

A halin da ake ciki kuma a Bamako ana sa ran masana za su kammala tsara wani shiri na aikewa da sojoji arewacin Mali.

Ranar 12 ga watan Octoba ne dai Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wani kudiri na aikewa da sojoji kasar Mali.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.