BBC navigation

Dasuki: Boko Haram na da alaka sosai da kungiyoyin 'yan ta'adda na Sahel

An sabunta: 5 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:44 GMT

Mai bawa shugaban Najeriya shawara ta fuskar tsaro, Kanar Sambo Dasuki (mai ritaya), ya ce ana dada samun alaka tsakanin 'yan kungiyar Jama'atu Ahlussunah Lidda'awati Wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram da kuma kungiyoyi masu tsatstsauran ra'ayin Islama a nahiyar Afrika.

Dasuki ya sanar da hakan ne a wani taron da aka yi yau kan ta'adanci a Abuja.

Ya ce babban abinda ya damu gwamnatin Najeriya shine karin hadin-gwiwar da a ke samu tsakanin 'yan kungiyar ta Boko Haram da kuma kungiyoyin 'yan ta'adda da su ka riga su ka kafu a yankin Sahel.

To amma bai yi karin bayani akan irin alakar da ya ce su na da ita ba.

Shi ma Mataimakin shugaban Najeriya, Namadi Sambo, ya ce gwamnati ta bullo da wasu sabbin matakai na yaki da ta'addanci.

Wata sanarwa da ta fito daga ofishinsa ta ce gwamnatin kasar ta yi la'akari da sarkakkiya da kuma yadda ta'addancin ke sauyawa a kasar.

Mataimakin shugaban kasar ya ce matakan za su maida hankali ne wajen ba jama'ar kasar fifiko, kamar yadda dokokin kasar suka shimfida.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.