BBC navigation

Ansaruddin ta bukaci gwamnatin Mali da kuma wasu kungiyoyin mayaka su rungumi sulhu

An sabunta: 6 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:09 GMT
Mali

Ana tattaunawa da Kungiyar Ansaruddin ta Mali

Babbar kungiyar 'yan kishin Islama wacce ta mamaye arewacin Mali, ta nesanta kanta da duk wani nauyi na tsattsauran ra'ayi da kuma ayyukan ta'addanci.

Kungiyar Ansaruddine ta bukaci gwamnatin Mali da kuma wasu kungiyoyin mayaka su rungumi sulhu, biyo bayan tattaunawar kungiyar da mai shiga tsakani wato shugaba Blaise Compaore na Burkina Faso.

Wannan sanarwar na zuwa ne a dai dai lokacin da shugabannin rundunonin sojin kasashen yammacin Afrika ke ganawa a Bamako a kan batun amfani da karfin soji a arewacin kasar, makawanni bakwai bayanda mayakan Islama su ka kwace yankin.

An dorawa kungiyar Ansaruddinne alhakin kashe mutane a bainar jama'a da kuma guntule wa wasu hannu.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.