BBC navigation

Gashu'a: anyi musayar wuta

An sabunta: 6 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:40 GMT

Harin da aka taba kaiwa a jihar Yobe

Rahotanni daga garin Gashua dake arewacin jihar Yobe a Najeriya sun ce an yi ta ɗauki- ba-daɗi tsakanin jami'an Rundunar Haɗin Gwiwar Samar da Tsaron jihar JTF, da wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan ƙungiyar nan ce da ake ƙira Boko Haram.

Mazauna yankin sun ce sun fara jin ƙarar harbe-harbe tun kafin asubahi, har ya zuwa wayewar garin yau, inda ƙarar tashin bama- bamai suka biyo baya.

Rundunar ta JTF tace ta samu nasarar hallaka 'yan bindigar huɗu tare da cafke ƙarin huɗu yayin arangamar.

Jihar Yobe dai na daga cikin jihohin arewacin Najeriya dake fama da tashin hankali da ake dangantawa da kungiyar Boko Haram.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.