BBC navigation

Wasu manyan sojin Syria sun sauya sheka zuwa Turkiyya

An sabunta: 6 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 17:07 GMT
Syria

Wsau manyan Sojojin syria sun sauya sheka

Kamfanin dillancin labaran Turkiya, ya ce Janar-Janar din soja su bakwai na rundunar sojin Syria, sun sauya sheka zuwa Turkiya.

Kamfanin na Anatolia, ya ce Janar-Janar din sun tsallaka iyaka ne tsakanin Syria da Turkiya, kuma an kai su wani sansanin 'yan gudun hijira dake Hatay, inda ake ajiye sojojin da su ka canja sheka, cikin tsauraran matakan tsaro.

'Yan Kasar Syria fiye da dubu dari daya ne su ka nemi mafaka a Turkiyya, tun bayan da aka fara rikici a kasar a cikin watan Maris na bara.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.