BBC navigation

Yau ake zaben shugaban kasar Amurka

An sabunta: 6 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:47 GMT

Obama da Romney

A kasar Amurka, 'yan takarar shugabanicin kasar na kammala yakin neman zabensu, inda ake sa ran masu zabe za su fara kada kuri'unsu ranar Talata.

Kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta baya-bayan nan wacce jaridar Washington Post da gidan talabijin na ABC News suka gudanar ta nuna cewa Shugaba Obama na gaban abokin hamayyarsa, Mitt Romney, da maki uku.

Kashi hamsin cikin dari na mutanen da ake sa ran za su kada kuri'unsu sun bayyana cewa za su goyi bayansa.

Shi kuwa Mitt Romney, kashi arba'in da bakwai ne suka ce za su zabe shi.

Sai dai an bayar da sanarwar cewa Mista Romney zai ci gaba da yakin neman zabe har zuwa ranar Talata.

A jihar Virginia, Mista Romney ya yi kira ga magoya bayansa da su shawo kan mutanen da ba su rigaya sun yanke shawarar wanda za su zaba ba.

Ya ce,"Mai yiwuwa wadansu 'yan uwanku da abokanku ba su yanke shawarar wanda za su zaba ba. Ku gaya musu su yi nazari kada su yi aiki da surutai''.

A jihohin da mahaukaciyar guguwar nan ta Sandy ta yi wa barna kuwa, hukumomi ne suka ce za su bar masu kada kuri'a su yi zabe ta hanyar email, ko fax saboda fargabar cewa wadansu masu kada kuri'ar ba za su iya zuwa rumfunan zabe ba.

Sai dai masana na fargabar cewa kada kuri'a ta wadannan hanyoyi ka iya kawo cikas ga zaben kasar, domin kuwa masu satar shiga shafin internet ka iya yin amfani da irin wannan dama wajen lalata kuri'un.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.