BBC navigation

Bene ya rufta kan mutane da dama a Accra

An sabunta: 7 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 16:44 GMT

Wani babban benen shagunan saye-da-sayarwa a Accra, babban birnin kasar Ghana, ya rufta a yayinda wasu ma'aikata da dama suka makale a ciki.

Rahotanni sun ce akalla mutane ukku sun mutu a yayinda a ka zakulo wasu da dama wadanda suka samu raunuka a baraguzan ginin na Melcom dake tsakiyar birnin.

Kuma ana fargabar cewar watakila akwai mutane kusan hamsin a cikin ginin a lokacin da ya rufta.

Shugaban kasar, John Dramani Mahama, ya dakatar da yakin neman zabensa, sannan kuma ya jajintawa wadanda lamarin ya rutsa dasu.

Kawowa yanzu masu aikin ceto sun ceto mutane 22; an kuma kaisu asibiti, inji wani jami'in 'yan sanda.

Ya ce a na ci gaba da kokarin ceto sauran mutanen da abin ya rutsa da su.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.