BBC navigation

'An kashe mutane da dama a Syria'

An sabunta: 7 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:36 GMT

Wadansu 'yan tawayen Syria

'Yan tawaye a kasar Syria sun ce an kashe mutane da dama kuma an jikkata wadansu a wani fadan da aka shafe sama da sa'oi hudu ana yi tsakanin sojojin gwamnati da masu adawa da Shugaba Bashar al-Assad.

Mutane akalla goma ne suka mutu a wadansu hare-haren bom da aka kai birnin Damascus, daya daga cikinsu a unguwar da tsiraru 'yan darikar Alawite ta Mista Assad suka fi rinjaye.

An harbe dan uwan shugaban Majalisar Dokoki har lahira a Damascus, mutum na baya-bayan nan a jerin kashe-kashen da ake yi na mutanen da ake burin samu a cikin magoya bayan Mista Assad.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.