BBC navigation

Obama ya lashe zaben Amurka

An sabunta: 7 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:23 GMT
Shugaba Obama

Shugaba Barack Obama na Amurka ya sake lashe zaben Amurka karo na biyu bayan ya kayar da abokin hamayyar sa Mitt Romney.

Yayin da aka bayyana sakamakon akasarin jihohi, Obama ya samu fiye da kuri'u 270 na masu zaben shugaban kasa wato electoral college domin lashe zaben shugaban kasar.

Obama ya samu nasara ne duk da rashin jin dadi da 'yan kasar da dama suka nuna game da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.

Shugaba Obama ya samu gagarumin rinjaye a jihohin da jam'iyyar sa ta Democrat ke da rinjaye, yayin da ya kuma samu nasara a wadansu daga cikin jihohin da aka fafata a cikinsu.

Shi kuwa abokin hamayyarsa, Mitt Romney, ya samu nasara a jihohin North Carolina da Indiana jihohi biyu da shugaba Obama ya lashe a zaben da ya gabata.

Godiya

Shugaba Obama ya gabatar da jawabinsa na samun nasarar zaben a jihar sa ta Chicago, inda ya mika godiya ga dimbin magoya bayansa da suke murnar nasarar da ya samu.

Ya kuma mika godiya ga abokin hamayyar sa Mitt Romney saboda yakin neman zaben da suka gudanar cikin tsanaki.

"Mu iyali guda ne a Amurka, muna fadi tashi tare a matsayin kasa guda", in ji Obama.

Ya kuma yi alkawarin aiki tare da shugabannin 'yan jam'iyyar Republican a Majalisar Wakilan kasar don rage yawan bashin da ake bin kasar da kuma yin garanbawul ga tsarin shige da ficen bakin kasar.

A shalkwatar yakin neman zaben abokin karawarsa Mitt Romney kuwa, dan takarar na jam'iyyar Republican ne ya taya shugaba Obama murnar nasarar da ya samu.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.