BBC navigation

Za a nada Bishop na Durham a matsayin sabon Archibishop na Canterburry

An sabunta: 8 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:15 GMT
Archibishop na Canterbury Roman William

Za a nada Justin Werlby sabon Archibishop

Za a nada Bishop Na Durham, Justin Werlby a matsayin sabon Archibishop na Canterburry, watau jagoran Kiristoci mabiyar darikar Anglican na duniya.

Ana sa ran a gobe Juma'a ne za a bada sanarwar nada shi a wannan mukami a hukumance.

Bishop Welby, wanda tsohon babban ma'aikacin wani kamfanin mai ne, ya zama Bishop ne a shekarar 1992, kuma ya samu mukamin Bishop na Durham din ne shekara guda da ta gabata.

Yana adawa da auren jinsi daya, amma yana goyon bayan a nada mata a matsayin Bishop.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.