BBC navigation

Kamaru da kamfanin Hydromine INC na Amurka sun kulla wata yarjejeniya

An sabunta: 8 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 18:18 GMT
Shugaba Paul Biya

Za a gina karin madatsun ruwa a Kamaru

Gwamnatin Kamaru da kuma kamfanin Hydromine INC na kasar Amurka sun sa hannu a kan wata yarjejeniya da za ta ba da damar yin nazari a kan wasu shirye-shirye na gina wasu tashoshin samar da wutar lantarki guda biyu, a yankin gabar teku da kuma Adamawa.

Saboda haka za a kashe Kudi CFA billiyan 600 a tsawon watanni 18 da za ayi ana gudanar da aikin nazarin .

Ana saran madatsun ruwan biyu zasu samar da guraben ayyukan yi sama da dubu goma sha shida

Ana kuma sa ran fara aikin gina madatsun ruwan a shekara ta 2018.

A yanzu haka dai ana cigaba da fama da karancin makamashin wutar lantarki a wasu sassan Kasar ta Kamaru

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.