BBC navigation

Shugaba Hu Jintao ya gargadi Shugabanni China kan cin hanci

An sabunta: 8 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:07 GMT

Shugaba Hu Jintao

Yayinda China ke shirin zabar sabbin shugabanninta, shugaba mai ci Hu Jintao ya yi gargadin cewa matsalar cin hanci da rashawa na yin mummunar barazana ga jam'iyyar kwaminisanci mai mulki da ma kasar baki daya.

A jawabin bude Babban taron jam'iyya a birnin Beijing, Mr Hu ya amsa cewa jamaa sun harzuka saboda matsalar ta cin hanci ta yi katutu a kasar:

Ya ce, "akwai bukatar a wayar da kan jama'a game da dokokin yaki da cin hanci da sauye-sauyen da muke kawo wa a fanonin daban-daban.

Muna bukatar mu kyautata dokokinmu na yaki da cin hanci da rashawa."


Sauyin shugabancin da za a kawo a kasar dai ya ci karo da zubar da mutuncin dan siyasar nan da ya yi tashe , Bo Xilai, wanda ya kasance da hannu a wani abun kunya na kisan kai da cin hanci da rashawa.

Taron wanda za a shafe mako guda ana yi wanda zai kawo karshen mulkin Hu Jintao zai mika mukaminsa na Shugaba ga wanda ake tsammanin zai gajeshi, XI Jinping.

Shugaba Hu Jintao ya ce kasar China za ta hukunta duk wanda aka samu da laifin cinhanci da kuma hawan kawara ga mulkin kasar.

Wakilai dubu biyu da dari uku da ashirin da biyar ne ke wakiltar mambobin Jamiyyar miliyan tamanin da biyu a wurin taron.

A wajen taron ne kuma za a amince da sabon kundin tsarin mulkin Jamiyyar da kuma zaben sabon kwamitin ladabtarwa.

Irin wannan babban taron na Jam'iyyar dai ana gudanar da shi ne duk shekaru biyar amma wannan karon ya ja hankalin mutanen kasar da kuma duniya baki daya saboda yawancin manyan shugabannin za su sauka bayan taron.

Taron zai ba da haske kan tsare-tsaren harkokin wajen kasar da sababbin shugabannin za su aiwatar da kuma yadda za su tunkari rashin jituwa da makwabtanta na yankin Asia da kuma hurdar kasuwanci da Amurka da ma Nahiyar Afirka.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.