BBC navigation

Girka ta amince da matakan tsuke bakin aljihu

An sabunta: 8 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:50 GMT

Shugaban kasar Girka, Karolos

Majalisar dokokin kasar Girka ta amince da matakan tsuke bakin aljihun gwamnati da kankanin rinjaye.

Ana bukatar daukar matakan ne dai, don samun wani tallafin ceto tattalin arzikin kasar daga kasashen ketare.

Matakan sun hada da rage kudaden fansho sosai, da kuma kara haraji, inda dokar ta samu nasara da rinjayen kuriu uku kacal.

Shugaban kasar Girka Antonis Samaras ya ce, idan Girka ta amince da wannan dokar za ta fita daga kangin matsalar tattalin arzikin da take fuskanta.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.