BBC navigation

Uwa ta sanya wa tagwayenta Obama da Romney

An sabunta: 8 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 18:29 GMT
Millicent Owuor

Millicent da 'ya'yanta

Millicent Owuor 'yar kimanin shekaru 20 da haihuwa, ta haihu ne a kudu maso yammacin kasar Kenya a ranar da aka sake zaben Obama a matsayin shugaban kasar Amurka a karo na biyu.

Matar dai na zaune a wani kauye kusa da kauyen su Obama inda adai-dai lokacin da ake murnar samun nasarar sa ne ta haifi tagwayen nata.

Millicent ta ce "Na sanya wa tagwayen sunayen ne saboda tunawa da ranar da aka gudanar da wannan zabe mai dimbin tarihi."

An dai haifi mahaifin shugaban kasar ta Amurka ne a Kenya, kuma matar kakan Obama har yanzu tana raye tana kuma zaune a wannan kauye mai suna Kogelo.

Mazauna Kogelo sun yi ta rawa da waka bayan an ayyana Obama a matsayin wanda ya lashe zaben Amurka da aka gudanar a Talatar da ta gabata.

Sarah Obama 'yar kimanin shekaru 90 a duniya ta ce "Obama ya yi nasara ne saboda Allah ne ya bashi, abu na biyu kuma yana kaunar jama'a, bai san banbanci ba."

Mahaifin Obama ya mutu a shekarar 1982

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.